Posts

Hausa da Hausanci a Ƙarni na 21 – Ƙalubale da Madosa

Hausa da Hausanci a Ƙ arni na 21 – Ƙ alubale da Madosa Abdalla Uba Adamu www.auadamu.com Department of Informationand Media Studies Faculty of Communications Bayero University, Kano, Nigeria Gabatarwa A duk fa ɗ in tarayyar ƙ asar Najeriya, babu al’ummar da ta fi ta Hausawa samun ƙ alubale a kan salsalarta da rayuwarta. Ba wani abu ne ya janyo haka ba illa albarkar da Allah Ya yi wa Hausa da Hausanci, ya zamanto ko ƙ a ƙ a mutum wanda ba Bahaushe ne ba ya yi gogayya da Hausawa, ya iya Hausa, to shi kam zai ɗ auki kansa ne a matsayin Bahaushe. Wannan ya sa ɓ a da yadda shi Bahaushen ya kan ɗ auki kansa, domin komai jimawar da ya yi a wani wuri, to shi har abada a matsayin Bahaushe zai ɗ auki kansa, ba ɗ an mazauna wurin ba. Abin da ya janyo haka kuwa shi ne ganin yadda ƙ asar Hausa ta zama da ɗ a ɗɗ iyar cibiyar ciniki tsakanin ba ƙ a ƙ en fatan Afrika na Sudan da kuma Larabawa, wanda ya sa ƙ asar Hausa ta zama wajen zaman mutane da ƙ abilu da yawa dom